1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Najeriya: Jihar Borno ta amince da dokar kare yara

January 11, 2022

Gwamnatin jihar Borno da ke Najeriya ta samar da dokar kare hakkin yara da cin zarafin dan Adama bayan kwashe tsawon lokaci ana cece-kuce kan wannan kudiri da wasu ke ganin zai iya taba al’adu.

https://p.dw.com/p/45NaB
Nigeria yara 'yan makaranta
Hoto: Afolabi Sotunde/Reuters

Gwamman jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya rattaba hannun kan kudirin kare hakkin yara wanda ya zama doka da ake fatan zai kyautata rayuwar yara da kare hakkin dan Adama a jihar. Wannan na nuna ke nan daga yanzu rashin sa yara a makaranta ko kuma amfani da yara wajen ayyukan kwadago da sauran abubuwan da ke zama cin zarafin yara laifi ne da zai iya haifar da hukunci mai tsananin kamar yadda gwamnatin ta fayyace a cikin wanann doka.

Kwamishinan Shari'a na jihar Borno Barista Kaka Shehu Lawan ya yi karin bayanin kan wannan doka da ma abun da ta kunsa don kare hakkin yara. Kafin samar da wannan doka ana samun yawaitar cin zarafin yara da kuma hana su karatu ko kasa ba su kulawa ta lafiya da ake ganin za a samu saukin haka da wanann doka.

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin yara su ka bayyana farin ciki kan samar da wannan doka da suka kwashe lokaci suna fatutukar ganin an tabbatar da ita ta zama doka. To sai dai iyaye da wasu bangarorin al'umma na ci gaba da nuna damuwa saboda yadda suke ganin wannan doka za ta iya karo da tsari gami da hukunce-hukunce na addini. Aiwatar da wannan doka za ta taimaka gaya a wanann jihar saboda yadda ake da yara da dama da rikicin Boko Haram ya jefa cikin mawuyacin hali da wasu ke amfani da halin da suke ciki suna jefa su ayyukan kwadago.