1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Baje kolin litattafai da rubuce-rubuce a Najeriya

Mohammad Nasiru Awal AH
September 24, 2019

A birnin Kaduna da ke arewacin Najeriya an kammala tarukan baje kolin al'adu da fasahar litattafai da rubuce-rubuce karo na uku wato Kabafest. Wannan shi ne batun da shirin Taba Ka Lashe ya duba.

https://p.dw.com/p/3Q9VO
Nigeria Kaduna | Buch und Kunstfestival Kabafest | Panel
Hoto: DW/I.Yakubu

Fitattun marubuta litattafan soyayya a arewacin Najeriya sun yi tilawar halin da rubuce-rubucen Hausa na soyayya ke ciki. Litattafan soyayya sama da 5,000 ne aka yi kokarin tilawarsu. Sai dai wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu matsaloli ke barazana ga adabin Hausa. An dai kwashe tsawon kwanaki hudu ana yin tarukan na baje kolin litattafai da fasahohi na rubuce-rubuce, taron kuma da aka kammala a ranar Asabar da ta gabata daya da cikin batutuwan da suka dauki hankali a taron na bana da ke zama karo na uku, shi ne batun adabin Hausa.