An halaka mutane da dama a kudancin Kaduna
August 7, 2020Talla
Wani mai suna Luka Biniyat, kakakin hadin gwiwar kungiyoyyin fararen hula a yankin, ya shedawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP da cewar adadin mamatan ka iya zarta wadanda hukumar 'yan sandan jihar ta bayar daga 21 zuwa 33. Ko baya ga mamatan dai rahotanni daga yankin sun ce an samu akalla mutun uku da suka ji rauni a yayin harin, kana kuma tuni aka kafa dokar tabaci a yankin.
Duk da yake ba wata kungiyar da tafito fili ta dauki alhakin klai harin, shaidun gani da ido sun tabbatar da manema labarai da cewar wasu mutane ne kan babura dauke da muggan makamai suka kaddamar da hare-haren a kauyuyukan biyar galibinsu mabiya addinin Kirista a karamar hukumar Zangon Katab.