1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Majalisa ta gaza amincewa da kasafin kudi

UbaleMusa/MNAMarch 17, 2016

A karo biyu cikin tsawon wata guda majalisun tarrayar Najeriya biyu sun gaza kaiwa ga amincewa da kasafin kudin kasar na bana.

https://p.dw.com/p/1IEtM
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Majalisun dokoki biyu na Najeriya sun fito don ban hakuri a bisa ga gaza cika alkawarin da suka dauka na amincewa da kasafin kudin bana a ranar Alhamis (17.02.2016). 'Yan majalisar dai sun ambata hakan ne a wani taro na manema labarai da suka yi a Abuja, inda suka shaidawa duniya dalilinsu na dage amincewa da kasafin.

Sanata Sabi Abdullahi da ke zaman kakakin majalisar datttawan Najeriyar ya ce kura-kuran da ke iya jawo matsala kan kasafin ne ya sanyasu jinkirta amincewa da shi sai dai al'ummar Najeriya na cigaba da nuna damuwarsu kan wannan jan kafa da ake yi game da amincewa da kasafin kudin da majalisun biyu ya kamata su yi.

Nigeria Abuja Präsident Muhammadu Buhari
Shugaba Buhari ya yi alkawarin kawo sauyi a NajeriyaHoto: picture-alliance/dpa/W. Krumm

Sai dai 'yan majalisun suka ce suna kokari ne wajen toshe dukannin wata hanya da suke ganin za a yi amfani da ita wajen wajen satar kudin gwamnati a irin wannan yanayi kamar yadda aka saba gani a kasafin kudin shekarun da suka gabata.

A cikin watan Disamban bara ne dai shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin na Najeriya da yawansa ya kai na naira triliyan shida da doriya a matsayin wanda ya ce da shi ne zai yi amfani wajen kawo sauyi a kasar wanda ya yi alkawari lokacin da ya ke zawarci kuri'unsu a wurare daban-daban da ya yakin neman zabe.