1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yin sulhu da 'yan bindiga a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
February 24, 2021

A kokarin lalubo hanyar shawo kan matsala ta satar mutane da garkuwa da su domin neman kudin fansa, kungiyar gwamnonin Najeriya ta amince da bin hanyar sulhu da masu kai hare-haren.

https://p.dw.com/p/3poQF
Afrika Nigeria Schulkinder freigelassen
Dalibai 'yan makaranta ma ba su tsira ba daga masu sata tare da garkuwa da mutanenHoto: Yusuf Ibrahim Jargaba/DW

Daukar wannan mataki da kungiyar gwamnaonin Najeriyar ta yi dai, ya nuna bayar da kai bori ya hau a kan bukatar rungumar sulhu domin shawo kan matsalar garkuwa da mutane da kai hare-hare da kisan ba gaira da ake zargin makiyayan da aikatawa a Najeriyar, ya zo ne bayan sabanin ra'ayi da wasu gwamnonin da ke adawa da batun sulhu balle batun afuwa.

Karin Bayani:Rikicin Fulani da Makomar kiwo a Najeriya

Kungiyar dai ta ce dagewa da amfani da karfi kadai ba zai zamo mafita ba, a saboda haka akwai bukatar hadawa da matakin sulhu. Kayode Fayemi shine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriyar: "Rungumar hanyar sulhu in ya zama dole ba mu da zabi, domin za mu yi duk abin da za mu iya mu shawo kan wannan matsala. Dole mu lalubo dalilin wannan matsala domin abin da muke fama da shi ta'adanci ne ba wani abu ba. Za mu iya kiransu masu daukar makamai ko garkuwa da mutane. Wannan gyauron matsalolin da muke fama da su ne a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, ko ISWAP ne ko Albarnawi ko kuwa na bangaren Shekau dukkaninsu gyauron abubuwan da muke fama da su ne".
Gwamnonin jihohin Zamfara da Katsina ne dai kan gaba wajen amfani da sulhu da makiyayan da ke kai hare-hare a Najeriyar, matsayin da ya fuskanci suka daga wasu gwamnoni irin Nasir Ahmad el-Rufai na jihar Kaduna. A baya dai an fuskanci cikas ko kuwa saba alkawari a kan sulhu da masu kai hare-haren musamman a jihar Katsina da ma wasu al'ummu a jihar Kaduna, ya sanya tunanin ko amfani da sulhun da ma ayyana masu kai hare-haren a matsayin 'yan ta'adda zai iya yin wani tasiri.

Cartoon Nigeria Sicherheit Lage
Gwamnonin Najeriya sun amince da yin sulhu da 'yan bindiga

Karin Bayani: Makomar Fulani a kudancin Najeriya

Tuni dai babban mamalin addinin Musulumci a Najeriyar Sheikh Ahmed Gumi ya yi nisa wajen yin kira da ma shiga tattaunawa da masu kai hare-haren, a kan batun sulhun da ma yi musu afuwa, batun da har yanzu ake jiran ganin matakin da gwamnatin Najeriyar za ta dauka.