1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kin zuwa yin gwajin corona a Najeriya

Muhammad Bello LMJ
January 19, 2021

Kwararru a harkokin lafiya a Najeriya na nuna damuwa kan yadda jama'a da dama ba sa bayar da hadin kai ga yadda ake kokarin shawo kan annobar corona a kasar, inda su ke kin zuwa gwaji.

https://p.dw.com/p/3o8b6
Südafrika Corona-Pandemie Johannesburg
Al'umma ba sa zuwa gwajin coronavirus yadda ya kamata a NajeriyaHoto: Luca Sola/Getty Images/AFP

Gwaje-gwajen da Cibiyar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta kasar NCDC ta gudanar tun bayan bullar annobar a Najeriyar kawo yanzu dai, bai wuce kan mutane miliyan daya da dubu 154 da 138 kwatankwacin mutane 5,439 a cikin mutane miliyan daya, wanda hakan ya sa Najeriyar ta fada jerin kasashen da har yanzu suna zamowa kurar baya ,a kokarin yin gwaje gwaje ga jamaar su.

Kwararru dai a harkokin lafiya a kasar na ci gaba da nuna damuwar cewar al'ummar kasar na yin sanyin kafa wajen kai kansu a gwada sannan wadanda sukai mu'ammula da wadanda suka kamu da annobar ta corona na yin kememe wajen zuwa cibiyoyin lafiya su tantance halin da suke ciki, yanayin kuma da kwararrun suka ce na dada assasa bazuwar annobar a kasar.

Karikatur Die 2. Corona-Welle in Nigeria
Corona ta sake dawowa a karo na biyu

Cibiyar ta NCDC ta ce adadin wadanda ke kamuwa da cutar na karuwa, tun satin karshe na watan Disambar da ya gabata. Boss Mustapha shi ne shugaban kwamitin shugaban kasa na sa ido da bayar da bayanai kan halin da ake ciki game da annobar ta COVID-19 a kasar da nufin ankarar da cibiyoyin kula da lafiya a wajen daukar matakan da suka kamata. A wani jawabi da ya yi, ya nunar da cewa bisa la'akari da abin da ke faruwa a duniya na game da wannan annobar ta COVID-19 ya kamata a yi hattara, inda ya yi kira da ga gwamnatocin jahohi da su dage da wayar da kawunan jama'a ta hanyar amfani da shugabannin al'umma. Batu na baya-bayan nan dai, shi ne yadda kungiyar likitoci ta kasa ta bayyana cewar akwai hadari matuka a matakin hukumomi na barin yara su koma makarantu, ganin cewa annobar ta COVID-19 na kara tsananta.