Najeriya na asara mai yawa daga masu kin biyan haraji
January 25, 2014A wani abun dake zaman hada baki da nufin rushe talakawa, yawan kudin da babu iyaka ne dai ke karkata daga aljihun gwamnatin kasar ya zuwa ga na yan kasuwa sakamakon wani shirin sassaucin taimakawa yan kasuwa a tarrayar Najeriya. Ana musu kallo na arziki har ma ana kiran su da ma sa'a. To sai dai kuma sannu a hankali tana kara fitowa a fili cewar fa akwai karatun kwange cikin dukiyar sabbabin mammalakan tattalin arzikin kasar ta Najeriya.
Kama daga kamfanin Coscharis mai harkar motoci ya zuwa ga dan uwansa na Sahara Oil mai takamar makamashi dai sun amfana daga wani shirin sassauta harajin da ya jawowa gwamnatin mummuna ta asara na lokaci mai tsawo. Akalla Naira Trilliyan guda da milliyan kusan dubu dari hudu ne dake zaman kusan kaso 25 cikin dari na daukacin kudin shigar na shekara ne dai suka kai ga bin shannun sarki daga shekara ta 2011 zuwa ta 2013 sakamakon sassaucin da ya shafi wasu kamfanonin kusan 300, amma kuma ke tada hankula cikin kasar a yanzu haka.Tuni dai yayan majalisun tarrayar kasar dake bincike a kan batun ke kiran da sake cikin shirin gwamnatin kasar dake azurta yan kadan tare da mai da ragowar jama'ar gari mabarata. To sai dai kuma a fadar karamin ministan kudin kasar ta najeriya Dr Yarima Lawal Ngama dai matakin sassaucin ya taimakawa tattalin arzikin kasar ne maimakon gurguntashi.
Habbakar kamfanoni ko kuma kokari na gurgunta tattalin arzikin kasar ta najeriya dai ana kallon sabuwar manufar a matsayin wani yunkuri na sakawa siyasa da biyayya a wurin yan kasuwar kasar da sannu a hankali suka koma masu juya akallar manufofin tattalin arzikin kasar baki daya.
Akalla manyan yan kasuwar kasar kusan biyar ne dai ke cikin majalisar tattalin arzikin da ke da alhakin manofofi a gareta, abun da kuma wasu ke kallo na iya kama hanyar son rai ga matakai da zasu taimaki harka ta kasuwarsu kadai maimakon daukacin al'ummar kasar dake da buri na cigaba amma kuma ke rayuwa cikin kangin fatara.To sai dai kuma afadar Ngama sabuwar manufar ta shafi sarki bata ma kuma ware talakawan kasar dake sana'ar noma ba.
Abun jira a gani dai na zaman mafita a cikin sabuwar dabarar da a kankanen lokaci ta dora kasar cikin taswirar yan kalilan din dake takama da karuwar arzikin da babu kamata da kuma da yawar da suma ke fuskantar talaucin da ya wuce kima.