Najeriya na duba yiwuwar bada mafaka ga Yahya Jammeh
January 12, 2017Talla
Rahotanni daga Najeriya na cewa majalisar dokokin kasar na shirin tattauna batun yiwuwar kasar ta bai wa shugaban kasar Gambiya Yayha Jammeh mafaka.
Shugaban kwamitin kula da tsara dokokin cinikayya a majalisar dattawan Najeriya Emmanuel Yisa Orker-Jev ya bayyana hakan a wannan Alhamis a tashar talabijin din gwamnatin Najeriyar ta NTA inda ya ce majalisar ta dauki wannan mataki ne a wani yinkuri na neman hanyoyin shawo kan takaddamar siyasar bayan zabe da ta dabaibaye kasar ta Gambiya.
A baya dai Najeriya ta taba bayar da irin wanann mafaka ga tsohon Shugaba Laberiya Charles Taylor wanda amma ta kare da mika shi a hannun kotun hukuntan manyan laifukan yaki ta duniya.