Najeriya: Rashin lafiyar Buhari ya dau hankalin PDP
May 9, 2018Jam'iyyar ta PDP ta ce hakan ya nunar cewa Shugaba Muhammdu Buhari ba zai iya tafiyar da jagorancin na Najeriya ba, inda ta ce ofishin na shugaban kasa a baya ya yi ta yi wa 'yan Najeriya karya kan halin rashin lafiyar ta Shugaban kasar, wanda har ya zuwa yanzu ba a san abun da ke damunsa ba. Shugaban na Najeriya Muhammadu Buhari mai shekaru 75 da haihuwa, a baya ma dai ya shafe tsawon watanni sama da biyar yana zaman jinya a birnin London na Britaniya, sai dai kuma a rabnar Talata 08 ga watan nan na Mayu shugaban ya sake komawa asibitin, inda ake sa ran zai dawo a ran 12 ga wata.
Dama dai a makon da ya gabata shugaban na Najeriya ya sake tsawa a birnin na London bayan da ya fito daga wata ziyara a kasar Amirka inda ya gana da shugaban Amirka Donald Trump, amma dai fadar shugaban na Najeriya ta ce sake tsawar a birnin na London dalili ne na matsala daga jirgi, ba wai dan ganin likita ba.