Magance rikicin jam'iyyar APC a Najeriya
March 17, 2022A baya dai ya kafa tarihi iri na ko in kula a cikin harkokin jam'iyyar, kuma ya sa ido ya kalli kokarin kai ta zuwa gidan tarihi. To sai dai kuma daga dukkan alamu tura ta kai bango, ga shugaban Tarayyar Najeriyar da ke neman yin bulala a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar. Cikin wata wasikar da ya aike ga shugabanin gwamnonin APC dai, Buharin ya nemi daukacin 'ya'yan jam'iyyar da su goya baya ga shugabancin Mai Mala Buni da nufin samun nasarar babban taron jam'iyyar na kasa. Wasikar ta Buhari dai na zaman ta ba za ta, a cikin rikicin jam'iyyar da ta kalli shugabanci guda biyu kasa da makonni biyu ya zuwa babban taro na kasa. Wasikar kuma da ga dukkan alamu ke shirin karewa da kara farraka cikin jam'iyyar, maimakon sulhunta tsakani na masu tsintsiyar. Kyaftin Bala Jibril dai na zaman daya a cikin jiga-jigan jam'iyyar da kuma ya ce, matakin Buharin na kan babbar hanyar mai da tsintsiyar madaurinki daya. Tuni dai shugabancin Mai Mala Bunin ya soke wani taron majalisar zartarawar na kasa da shugaban rikon Abubakar Sani Bello ya tsara gudanarwar, abun kuma da ya harzuka 'yan kwamitin riko na APC da suka fitar da wata sanarwar korar sakataren jam'iyyar na kasa James Akpanudoedehe.
Abubakar Mai Kudi dai na zaman tsohon shugaban matasan jam'iyyar CPC na kasa kuma guda cikin jiga-jigan APC, wanda kuma ya ce matakin sallamar ta dace a kokarin wankan tsarki a cikin APC mai mulki. Akwai dai tsoron sake rincabewar sabon rikici, har a tsakanin gwamnonin da ke zargin shugaban kasar da kokarin daukar matsayi a cikin rikicin da ke kama da gwagwarmayar mallaki na ruhin jam'iyyar. Sake komawar Bunin na iya aiken sako na inda baki na shugaban kasar yake shiri ya karkata, a cikin neman samar da dantakarar da zai ja ragamar jam'iyyar APC a zaben shugaban kasar da ke tafe. To sai dai kuma a fadar Malam Garba Shehu da ke zaman kakakin shugaban kasar, babban burin Buharin na zaman daidaiton lamura cikin jam'iyyar da ke dada fuskantar barazana mai girma. A ranar Asabar ta makon gobe ne dai, aka tsara masu tsintsiyar za su gwada sa'ar iya kai wa ga sake samar da shugabancin kasa a cikin jam'iyyar, taron kuma da ke zaman zakaran gwajin dafi makomar jam'iyyar a nan gaba.