Shirin dogaro da iskar gas a Najeriya
September 14, 2023Akalla kafa triliyan 200 na iskar gas ne dai Najeriyar ke takama da shi, adadin da ya haura yawan man fetur din kasar tare da mai da ita kasa ta 12 da ke da albaraktun iskar ta gas a duniya baki daya. To sai dai kuma Najeriyar ta dauki shekaru kusan 60 ta na kone iskar da ke da tasirin gaske kuma ke iya sauya makomar kasar a lokaci kankani, kafin wani sabon mataki da a karkashinsa Abujar ta sanar da bai wa wasu kamfanoni na duniya izinin tace iskar tare da tabbatar da amfaninta a ciki da ma wajen Najeriyar.
A karkashin wannan sabon shirin dai, ana sa ran kamfanonin za su kula da ayyukan kare kone iskar ta gas cikin wasu filaye 49 na aikin hakar mai a kasar. Tun kusan shekaru shidan da suka gabata ne dai, Abujar ta fara kokarin shirin da ke da zummar kai karshen lalata muhalli ko bayan karin kudin shiga ga aljihun 'yan mulki. Akwai dai fatan karuwar wadatar iskar cikin kasa na iya kai wa ya zuwa rage farashi da kila karkatar da tunanin 'yan kasar da ke wayyo fetur. Koma ya zuwa yaushe ne miliyoyin 'yan Najeriyar ke iya kai wa ya zuwa gani cikin kokon sha a arziki n na kasar su dai, kame iskar tare da mai da ita zuwa ga arziki na shirin sauya da dama a cikin aljihun 'yan mulkin kasar.
Akalla kafa biliyan 8,000 na iskar ta gas Najeriyar take konawa a shekara, a wani abun da ke iya biyan daukacin bukatun wutar lantarki cikin kasar. Tuni dai da ma kasar tai nisa wajen shimfida wani bututu, daga sashen kudanci zuwa arewaci da nufin amfana daga iskar da ko bayan wutar ke iya amfani ga kamfanoni na kasar. Dakta Abubakar Atiku Koko dai na zaman kwararre na makamshi a jami'ar Usman dan Fodiyo da ke a Sokoto, kuma ya ce nasarar tace iskar na iya samar da kudin shigar da suka haura na man fetur da masu mulki ke dogaro da shi tsawon lokaci. Ya zuwa yanzun dai iskar ta gas na bai wa kasar kaso 65 cikin 100 na kudin shigarta, a dadin kuma da ke iya karuwa zuwa kusan kaso 80 cikin 100 bayan tace iskar.