1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin 2020

October 8, 2019

Sabon kasafin da ke zaman irinsa na farko cikin mataki na gaba an dora shi ne bisa dalar Amurka 57 kan kowace gangar man fetur da kuma hakar ganga miliyan 2.18 kowace rana.

https://p.dw.com/p/3QuUU
Nigeria Kabinett Muhammadu Buhari Präsident
Hoto: Reuters/A.Sotunde

A badin dai gwamnatin kasar ta ce za ta kashe Naira Triliyan 10 da miliyan dubu 330 domin manyan ayyuka da tafi da harkokin yau da gobe. Hankalin gwamnatin dai a cewar shugaban kasar zai karkata ne ga  kammala ayyukan da gwamnatin ta fara a sassa daban daban maimakon sabbi

“Hankalinmu zai karkata ne ga karasa ayyukan dake kasa maimakon sabbi. Ba'a yarda wata hukuma ko ma'aikata ta gwamnatin ta karbi wasu sabbin ayyuka cikin kasafin ba, har sai idan akwai cikakken tanadi na ayyukan a cikin kasafin Haka kuma mun tura duk manyan ayyukan da ba za'a iya kammalasu ba a shekarar bana zuwa kasafin badi“.

A badin dai gwamnati na sa ran samun kudin shigar da ya kai Naira Triliyan 8 da miliyan 155 a matsayin kudin shiga da mafi yawansu za su fito daga wani kari na harajin mai saye da gwamnatin ta sanar ta ke kuma shirin aiwatarwa daga shekarar da ke tafe.

Gwamnatin dai ta tsara kashe Triliyan 3.6 domin albashin ma'aikata a cikin sabon tsarin mafi karancin albashi.

Kasafin dake zaman irin sa na farko a lokaci mai nisa da ke da burin cika ka'idar kasafin kudin Janairu zuwa Disamba na nufin abubuwa daban daban a idanun ‘yan majalisun kasar daban daban.

Tarrayar Najeriyar dai na fatan kasafin zai taimaka wajen kara dadaito ga tattalin arzikin kasar wadda sannu a hankali ke kulle iyaka a matsayin sabuwar dabarar kai karshen tafiyar hawainiya ta tattalin arzikin.