Najeriya: Ba ma hada kai da Faransa
December 26, 2024A wata sanarwa da ministan yada labarai na Najeriya Mohammed Idris ya sanya wa hannu, gwamnatin ta ce wadannan zarge-zargen ba su da tushe bare makama kuma tunani ne kawai irin na Janar Abdourahmane Tchiani. Sanarwar ta gwamnatin Najeriya ta ce kasar ba ta taba hada kai da Faransa ko kuma wata kasa ba, domin daukar nauyin 'yan ta'adda don hargitsa Nijar a yayin da take mulkinta da ba na dimokradiyya ba. Yayin wannan zargin dai Janar Tchiani ya ce ba 'yan ta'addan yankin Tafkin Chadi kawai ake taimako da makaman ba, har ma da wadanda ke wasu jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya na kan iyaka da Nijar domin kai wa Nijar hare-hare da zummar hargitsa ta. Shugaban mulkin sojan Nijar din ya yi wannna zargin ne a wata hira ta musamman da ya yi a gidan radiyo da Talabijin na kasar na RTN, inda ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriyar da karbo kudi a wajen Faransan domin gudanar da wannan aiki.
Janar Tchiani ya ce kafin tabbatar da bayanan da suka samu daga wajen shugabannin 'yan ta'adda kan abin da Faransan ke kitsawa, sai da suka tuntubi hukumomin Najeriya wadanda suka aiko da jami'ansu Jamhuriyar ta Nijar suka tattauna da 'yan ta'addan kan wannan batu. Sai dai ya ce bayan jami'an Najeriyar sun koma gida, babu wani mataki da suka dauka. Haka kuma, Janar Tchiani ya zargi shugabannin kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO da Shugaba Tinubu na Najeriya da kasancewa 'yan amshin shatan Faransa da ya ce suna zuwa su karbo kudi a hannunta, domin taimaka mata ga cimma muradanta na ruguza kasashensu. Ya kuma ce sun samu bayanai da ke tabbatar masu da cewa a baya-bayan nan ma Faransa ta samar da bindigogogi ga 'yan Boko Haram, a fafatawar da suke da sojojin Chadi, domin su harbo jiragen yaki a yankin Tafkin Chadin. Yanzu haka dai wadannan zarge-zarge da Shugaba Tchiani ya yi ga Faransa da shugabannin wasu kasashe makwabta sun haifar da muhawara a kasar, inda wasu ke nuna gamsuwarsu da duk abubuwan da ya fada wasu kuma ke cewa suna bukatar shugaban ya ba su hujjoji na zahiri a kasa ba zargi na fatar baki ba.