1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Kalubalen sauya fasalin kudin Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 17, 2023

Babban bankin Najeriya wato CBN ya karyata labarin cewa ya bayar da izinin ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudi na Naira 1000 da 500.

https://p.dw.com/p/4Nffl
Najeriya | Naira | Babban Banki
Karin wahala kan sauya fasalin kudin NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Cikin wata sanarwa ne babban bankin na Najeriya CBN ya musanta wannan batu, inda ya bukaci kafafen yada labarai da su rinka tabbatar da labari kafin su yada shi. Wakilinmu na Abuja Uwais Abubakar Idris ya ruwaito cewa, tun da fari an rinka yada wasu labarai a kafafen sada zumunta na zamani na kasar da ke nuni da cewa babban bankin Najeriyar ya umurci kananan bankuna da su ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudin na 500 da kuma dubu daya da tuni wa'adin karbar su ya cika. A wani labarin kuma jami'an 'yan sanda sun harba barkonon tsohuwa a kan masu zanga-zangar adawa da karancin takardun kudin, wadanda suka kawo tarnaki a harkokin kasuwanci a Lagos da ke zaman cibiyar kasuwancin Najeriyar. An dai kwashe tsawon lokaci ana fama da karancin sababbin takardun kudin Naira da babban bankin kasar CBN ya sauya fasalinsu, abin da ya jefa rayuwar al'ummar kasar da dama cikin garari. A Alhamis din da ta gabata dai Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar, yayin wani jawabi ya bukaci a ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudi na Naira 200.