Najeriya: Yaki da ta'addanci ta yanar gizo
March 8, 2017
Ita dai Ummukaltum Muhammad wanda aka fi sani da Kaltum ta kasance mai karacin shekaru da ta fito ta ke ganganmi domin wanzar da zaman lafiya a Maiduguri da sauran sassan jihohin Arewa maso gabashin Najeriya.
Ta na wannan gangami ne karkashin wata kungiya da ta bude mai suna Kaltume Peace Foundation a turance kuma tuni aka bata mukamin jakadiyyar zaman lafiyar jihar Borno.
Ta kuma fayyace manufar wannan ganganmi na ilmantar da mata matasa da ake yaudararsu da ko amfani da sunan addini wajen kai hare-hare na ta'addanci kamar dai yadda ta min bayani.
Matashiyar ta ce ta zabi amfani da kafafen sadarwar na zamani ne saboda yadda matasa suka mu'amala da su inda kuma ta ke fadada gangamin nata wajen amfani da sauran kafafen yada labarai.
Tuni matasa suka amsa kiran wannan matashiya abinda ake ganin zai taimakawa yaki dan magance matsalar tsaro a Najeriya.
Dr Abubakar Muhammad daya daga cikin matasan ne da suka rungumi wannan gangami na fadakar da mata masata domin a dai na amfani da wasu wajen kai hare-haren ta'addanci. Ya kuma ce tana nema tallafi daga dukkamin al'umma.