1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da daliban jami'a

August 17, 2024

Kimanin dalibai 20 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Benue da ke shiyyar tsakiyar arewacin Najeriya kamar yadda rundunar 'yan sanda ta sanar.

https://p.dw.com/p/4jZgT
Jami´ar Maiduguri da ke jihar Borno a Najeriya
Jami´ar Maiduguri da ke jihar Borno a NajeriyaHoto: Alamin Muhammed/DW

Daliban sun fito daga jami'o'in Maiduguri da ke Borno da na Jos da ke Filato wanda suka gamu da ibtila'in a yankin Otukpo da ke kasancewa mabuyar 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane, acewar mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Benue Catherine Anene, inda ta ce daliban da ke neman kwarewa a fannin kiwon lafiya na kan hanyarsu ta zuwa kudancin kasar domin halartar taron kungiyar dalibai likitoci ta kasa.

Karin bayani: Hare-haren kunar baklin wake sun salwantar da rayuka a Najeriya 

Arewacin Najeriyar dai ta yi kaurin suna wajen ayyukan 'yan bindiga da ke garkuwa da mutane domin samun kudin fansa da suke amfani da damar karancin jami'an tsaro wajen tare tituna da kuma kai wa kauyuka farmaki daga lokaci zuwa lokaci.

Karin bayani: A Najeriya 'yan bindiga sun tashi kauyuka da dama

Tuni dai kungiyoyin daliban kasar ke ci gaba da kiraye-kiraye ga hukumomi wajen tabbatar da lafiyan daliban tare kuma da kubutar da su cikin gaggawa.