Gurfanar da masu daukar nawin Boko haram
February 4, 2022Talla
Mahukunta a tarayar Najeriya bayan karban sakamakon wani bincike da aka gudanar a game da ayyukan ta'addanci da suka addabi kasar da ke yammacin Afirka, yanzu haka sun ce sama da kamfanoni 100 ne za su gurfanar a gaban kuliya bisa zarginsu da bayar da kudade don tallafa wa ta'addanci.
A sanarwar da ministan yada labarun kasar Lai Mohammed ya fidda a yammacin jiya, ya ce tuni aka damke mutane 45 daga cikin wadanda ake zargi.
Ministan yada labaran ya kara da cewar akwai sama da mutum 500 da idanuwan masu bincike ke kansu, da kuma wasu kamfanoni 123.
Wadannan mutanen da ma kamfanonin ana zarginsu da tallafa wa ayyukan mayakan Boko Haram da na IS ta kai tsaye ko kuma ta barauniyar hanya safarar kudade ba bisa ka'ida ba.