1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashe 7 za su samu tallafin miliyan 100

Abdul-raheem Hassan MNA
November 18, 2020

Ofishin kula da jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, ya ware dala miliyan 100 a matsayin agajin gaggawa domin taimaka wa kasashen da ke fama da barazanar yunwa da tashe-tashen hankula da kuma annobar Corona.

https://p.dw.com/p/3lV9n
Nigeria Landwirtschaft Bauern
Hoto: Luis Tato/AFP

Kasashen Najeriya da Afganistan da Burkina Faso da Kwango da Sudan ta Kudu da Yemen za su sami tallafin dala miliyan 80, wato kaso mafi yawa na kudin tallafin domin yaki da matsalolin karancin abinci da barazanar tsaro da suke fama da su. Najeriya za ta samu dala miliyan 15 ita kadai.

Habasha za ta samu ragowar dala miliya 20 saboda barazanar yunwa da kasar ke ciki, musamman yadda yankin arewacin Tigray ya sake fadawa sabon rikici.

Akwai hasashen sake fuskantar barazanar yunwa a Arewa maso gabashin Najeriya da Burkina Faso da Sudan ta Kudu da kuma kasar Yemen a karon farko tun 2017, bayan da aka samu matsalar yunwa a wasu yankunan Sudan ta Kudu.