NARTO: Yajin aikin motocin dakon mai a Najeriya
February 20, 2024Lagos ita ce cibiyar kasuwancin Nigeria, manyan motoci da ke sufuri zuwa jihohi kasar da motocin da ke jigilar man fetur duk sun kasance a ajiye.
koda yake Kungiyar masu motocin dakon kayan NARTO ta yi shelar tattaunawa da jamian gwamnati da kuma masu kanfanonin da ke muamala da wannan jigila amma har yanzu ana ci gaba da tattaunawa domin samun fahimtar juna a tsakani kamar yadda shugaban kungiyar ta NARTO Alhaji Yusuf Lawal Usman ya baiyana.
Karin Bayani: Karancin fetur ya kunno kai a Najeriya
Ya ce gaskiya ne yajin aiki na nan daram sai dai muna ci gaba da tattaunawa da kamfanoninmu domin samun mafita duk kuwa da cewa sun yi mana wani karin kudi amma dai akwai sauran rina a kaba
To sai dai a lokuta da dama masu fada aji da 'yan kasa talakawa kan yi tsokacin cewa talaka na kukan rashin abinci ko me ya kawo batun yajin aikin a yanzu.
Karin Bayani: Yawan cinikin man Najeriya ya ragu
Shugaban kungiyar ta NARTO Alhaji Yusuf Lawal Usma ya ce suna sane da halin matsi da ake ciki a Najeriya amma kuma har yanzu bukatun yau da kullum na samun nakasu amma dai za su ci gaba da tuntubar juna
Karin kudin man diesel na daya daga cikin hujjoji na shiga wannan yajin aikin. A jihar Oyo kuwa sai da talakawan gari suka fito kan tituna suna bore na tsadar rayuwa .