Nasarar ganawa tsakanin kasashen Koriya
January 9, 2018Talla
Ganawa tsakanin Koriya ta Kudu da Koriya ta Arewa ta haifar da abin da ake bukata, inda mahukuntan Koriya ta Arewa suka amince da tura wakilai zuwa gasar guje-guje da tsalle-tsalle na Olympics na hunturu a watan Febrairu wanda ita Koriya ta Kudu za ta dauki nauyi. Wannan ke zama ganawa ta farko tsakanin bangarorin biyu tun shekara ta 2015 kimanin shekaru biyu ke nan.
Ministoci daga bangarorin biyu suka jagoranci wakilai zuwa wajen wannan tattaunawa, kuma ita Koriya ta Kudu ta nemi amfani da wannan dama domin dakile zaman zullumi a mashigin ruwan Koriya, sakamakon matakin Shugaba Kim Jong-Un na Koriya ta Arewa kan bunkasa makaman nukiliya.