Nasarar masu zanga-zanga a Burkina Faso
October 31, 2014A cikin takaradar murabus din da fadar shugaban kasar ta fitar, Shugaba Blaise Campaore yace "a cikin burin da ya ke da shi na kare dimokradiyar wannan kasa, tare da tabbatar da zaman lafiya ya yi murabus da ga mukamin sa na shugaban kasar Burkina Faso". Sanarwar dai wani gidan talbijin mai zaman kansa a kasar na TB1 ne ya fitar da ita a wannan Juma'a. Saidai gabanin sanarwar, tuni wani kanar din sojan ya sanar wa da dubban al'ummar kasar da ta hallara a dandalin "Place da la Nation", cewa sun karbi mulki daga hannun Shugaba Campaore inda nan take wurin ya kaure da sowa, yayin da sauran al'ummar Wagadugu babban birnin kasar suka watsu cikin gari a kan ababan hawa su na nuna murnarsu ganin yadda hakarsu ta cimma ruwa.
Faransa ta yi na'am da murabus din
Tuni dai fadar shugaban kasar Faransa, kasar da ta yi wa Burkina Fason mulkin mallaka ta yaba da matakin da Campaore ya dauka tana mai cewa yin hakan zai dawo da kwanciyar hankali a cikin kasar, inda ta ce ta na goyon bayan yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasar, tare da mayar da hankali wajan shirya zabe na gari. Kawo yanzu dai babban hafsan-hafsoshin sojan kasar Janar Honoré Traoré ne ke rike da ragamar mulki, ko da yake a hannu guda da dama da ga cikin 'yan adawa da ma kungiyoyin farar hula da suka yi wannan zanga-zanga da basu yarda da shugabancin na shi ba.
Saidai ana iya cewa wannan mataki da aka cimma na murabus din shugaban kasar ta Burkina Faso cikin dan kankanin lokaci, na da nasaba da irin matsin lambar da ya fuskanta daga bengarori da dama. Ko da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ma dai da kungiyar ECOWAS da ma Tarayyar Afirka sun tura wakilai na musamman dan ganin an samu maslaha cikin kasar.
Idanu sun koma kan gwamnatin rikon kwarya
A yanzu dai a iya cewa kasashen duniya musamman ma na nahiyar Afirka sun zura idanu wajan ganin yadda kasar ta Burkina Faso za ta samu daidaito bayan murabus din shugaban kasar da tuni ya fuce zuwa garin PO dake iyaka da kasar Ghana. Ana kuma ganin hakan tamkar wata 'yar manuniya ce ga sauran Shugabannin kasashen Afirka masu irin wannan ra'ayi na neman canza kundin tsarin mulki, ko kuma shirya magudin zabe dan ci gaba da mulki. Yanzu dai ana jira aga yadda tattaunawar masu ruwa da tsakin kasar ta Burkina Faso za ta kaya dangane da samun amincewa da wanda zai zamo shugaban kasar na rikon kwarya.