Nasarar 'yan adawa ta janyo murna a Najeriya
April 1, 2015
A Najeriya nasarar da jagoran 'yan adawa Muhammadu Buhari ya samu na lashe zaben shugaban ya jefa jama'a cikin murna a sassa daban-daban na kasar. Buhari na jam'iyyar ACP ya zama dan adawa na farko da ya kayar da jam'iyya mai mulki a Najeriya, inda ya samu kimanin kashi 55 cikin 100 na kuri'un da aka kada, yayin da Shugaba mai-barin gado Goodluck Jonathan na jam'iyyar PDP ya samu kashi 45 cikin 100. Tuni Jonathan ya rungumi kaddara.
Da sanyin safiyar wannan Laraba shugaban hukumar zaben kasar mai zaman kanta Farfesa Attahi Jega ya cikekken sakamakon zaben.
Sabon Zabebben shugaban na Najeriya, Janar Muhammadu Buhari da ke zama tsohon shugaban gwamnatin mulki soji, ya yi takara sau uku a baya duk bai samu nasara ba. Dan shekaru 72 da haihuwa, ya yi jawabin samun nasara da safiwar wannan Laraba, inda ya tabbatar wa 'yan kasar shirinsa na kawo sauye-sauye.