NATO: Scholz ya yi maraba da girke makamai a Jamus
July 11, 2024Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya yaba wa matakin da Amirka ta dauka na girke makamai masu linzami da ke cin dogon zango a kasarsa domin nuna turjiya.
Olaf Scholz ya fada wa manema labarai a taron NATO da ake rufewa ranar Alhamis cewa abu ne na tabbatar da zaman lafiya da nuna turjiya sannan mataki ne mai muhimmanci a lokaci mafi dacewa.
Sabon firaminista ya yi alkawarin sake gina kasar
A ranar Laraba ce Amurka ta sanar da matakin karfafa NATO a Tarayyar Turai akan Rasha, ta hanyar fara girke manyan makamai masu linzami da ke cin dogon zango a Jamus daga 2026.
A martanin da ta yi kan matakin a wannan Alhamis, Rasha ta ce ta na shirin daukar matakin da ya dace domin dakile barazanar NATO.
Taron NATO na kwanaki uku yana gudana ne a kasar Amirka daidai lokacin da kungiyar tsaron ke cika shekaru 75 da kafuwa, inda yanzu take da mambobi 32, kuma take zama kawancen tsaro mafi girma da tasiri a duniya.