1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman Karbar Bakuncin Wasannin Olympics a 2012

May 17, 2004

A gobe talata idan Allah Ya kaimu za a ci gaba da tankade da rairaya domin tace biranen da zasu shiga mataki na gaba na takarar neman karbar bakuncin wasannin olympics a shekara ta 2012

https://p.dw.com/p/BvjX
Ministan cikin gida na Jamus Otto Schily mai nema wa birnin Leipzig damar karbar bakuncin wasannin Olympics a shekara ta 2012
Ministan cikin gida na Jamus Otto Schily mai nema wa birnin Leipzig damar karbar bakuncin wasannin Olympics a shekara ta 2012Hoto: AP

A dai halin da ake ciki yanzun birane tara ne suka rage daga cikin jerin biranen da suka shiga takarar neman shirya wasannin Olympics a shekara ta 2012. Wadannan kasashe sun hada da Rido de Janeiro a Brazil da Havana a Cuba da New York a Amurka da London a Birtaniya da Paris a Faransa da Istanbul a Turkiyya da Mosko da Rasha sai kuma Leipzig a nan Jamus. A gobe talata idan Allah Ya kaimu za a ci gaba da tace biranen, kafin a kai ga takara ta karshe a shida ga watan yulin shekara mai zuwa, domin tsayar da birnin da zai karbi bakuncin wasannin na Olympics a shekara ta 2012. Akwai tsayayyun ka’idojin da aka tanadar domin tace wadannan birane ta yadda mai yiwuwa ma dukkan biranen guda tara su tsallaka domin shiga takarar karshe a shekara mai zuwa. A gobe talata idan Allah Ya kaimu, shugaban kwamitin Olympics na Duniya Jaques Rogge zai ba da sanarwa game da sakamakon binciken da aka gudanar akan birnin da ya cika wasu sharudda na fasaha da aka tanadar domin tsallakewa zuwa mataki na karshe na takarar neman shirya wasannin na Olympics a shekara ta 2012. A dai wannan marra da muke ciki yanzu ba wanda ya san yadda zata kaya illa a yi hasasheb kawai, kamar yadda Klaus Lennartz, masanin tarihin wasannin Olympics ya nunar ya kuma kara da cewar:

Da farko dai sai in ce birnin Leipzig na da dama ce takashi 50 bisa 50 ta tsallakewa domin kaiwa ga matakin karshe a shekara mai zuwa. Idan har birnin na Leipzig ya tsallaka to kuwa sauran biranen ma zasu bi sau. A zamanin baya an shiga shawarar kayyade yawan masu takarar, amma ga alamu tuni aka dawo daga rakiyar wannan ra’ayi. A saboda haka, in har za a ci gaba akan haka to shi ma birnin na Leipzig zai kai matakin karshe. Amma idan za a yi tankade da rairaya ne to kuwa mai yiwuwa birnin ya kasance cikin jerin wadanda za a tankade su.

Amma fa ministan cikin gida na Jamus Otto Schily ba ya da irin wannan ra’ayi. A ganinsa wannan takarar ba ta shafi birnin Leipzig ne shi kadai ba, wata manufa ce ta kasa baki daya. Ministan ya gabatar da dukkan shirye-shiryen da gwamnati ta tanadar domin rufa wa birnin baya, lamarin dake da muhimmanci domin tsallake shingen na gobe talata. Bayan kai ruwa rana da aka sha famar fuskanta a watannin baya, mahukuntan birnin na Leipzig sun taka rawar gani wajen cika dukkan sharudda na fasaha da aka zayyana. Abu daya da ka iya zama karan tsaye ga birnin shi ne maganar masaukin baki. Domin kuwa ta la’akari da gaskiyar cewa Leipzig dan karamin gari ne, giggina kasaitattun gidajen otel ba ya da wani amfani dangane da ‚yan kwanaki kalilan da za a yi ana gudanar da gasannin na Olympics. Amma shawarar da aka tsayar domin tinkarar wannan matsala ita ce ta sabunta tsaffin gidaje da yi musu gyarar fuska domin aiwatarwa ra gajeren lokaci, lamarin da shi kansa shugaban kwamitin Olympics na Duniya Jacques Rogge ya yaba da shi. A yanzun dai sai kawai a zura ido a ga yadda zata kaya a gobe talatar idan Allah Ya kaimu.