Kawo karshen yakin Sudan ta Kudu
June 25, 2018Talla
Shugaba Omar al-Bashir na Sudan ne ke karbar bakuncin taron a Khartoum babban birnin kasar ta Sudan. An dai kwashe tsahon shekaaru hudu da rabi kawo yanzu ana gwabza fada tsakanin magoya bayan Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu da babban abokin hamayyarsa kana tsohon mataimakinsa Riek Machar a 'yar jaririyar kasar ta duniya, da ta fada yakin basasa jim kadan bayan samun 'yancin cin gashin kai daga Sudan. Wannan dai shi ne karo na biyu a sabon babin tattaunawar da aka bude tsakanin abokan hamayyar biyu, inda Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya karbi bakuncinsu a karo na farko a Addis Ababa bababban birnin kasar ta Habasha. Shugaba Omar al-Bashir na Sudan da takwaransa Yoweri Museveni na Yuganda na halartar taron sulhu.