Ina aka kawana a nazarin mulkin mallaka?
May 4, 2021Naita Hishoono daraktar cibiyar nazarin dimukuradiyya, na ganin tasiri mulkin mallakar Jamus a duk lokacin da take tattakawa a Windhuk babban birnin kasar Namibiya, akwai tituna masu sunan Jamusawa da kantunan Jamusawa da majami'ar Christ Church da aka gina zamanin mulkin mallaka.
Karin Bayani: Shekaru 100 bayan mulkin mallaka a Namibiya
Wani abin da ba a ganin fili amma kuma ke a zukatan mutane, shi ne kisan kare dangi da Jamusawa suka yi wa al'ummomin Herero da Nama. Kowa a Namibiya ya san wannan mummunan abin da ya faru a tarihin kasar. Sai dai abin ya bambanta lokacin da Hishoono ta zo Jamus: "'Yan Namibiya sun san tarihin mulkin mallaka, domin muna gani a tsarin gine-ginenmu, muna ganin tasirinsa a tattalin arziki. Saboda haka dangantaka tsakanin Jamus da Namibiya tamkar ya ce da kanwa, inda yar ta manta da abin da ya faru."
Gwamnatin Tarayyar Jamus ma ta san da haka kamar yadda karamar minista a ma'aikatar harkokin wajen Jamus, Michelle Müntefering ta nunar a gaban majalisar dokoki a watan Nuwamban bara: "Mun dade a Jamus muna yaudarar kanmu cewa ba mu da wani tabo na zamanin mulkin mallaka, domin mulkin mallakar da muka yi na gajeren lokaci ne da ba za a iya cewa an aikata wata ta'asa a ciki ba. Har yau kana jin wannan ikirari. Matsalar ita ce kullum muna maimaita abu guda."
Karin Bayani: Taƙaddama tsakanin Namibiya da Jamus
Daga baya ne dai Daular Jamus ta shiga jerin 'yan mukin mallaka, inda a shekarun 1880 Jamus ta mamaye wasu yankunan Afirka, amma ta rasa su bayan ta sha kashi a yakin duniya na daya. An kuma dauki tsawon shekaru 100 kafin wata gwammatin Jamus ta nuna aniyar amincewa da haka. A 2018 a cikin yarjejeniyar kafa gwamnatin kawance, jam'iyyun CDU/CSU da SPD sun amince su yi nazari a tarihin mulkin mallakar, domin har yanzu ana ganin tasirinsa ko da yake ba kowa ne ya san da haka a rayuwa ta yau da kullum ba. Akwai tituna ma su dauke da sunan Jamusawa da wuraren tarihi da ke yin tuni da ta'asar da Jamus ta aikata lokacin mulkin mallakar.
Jürgen Zimmerer masanin tarihin mulkin mallaka a birnin Hamburg na Jamus, ya ce da yawa cikin dalibansa ba su da masaniya kan batun: "Idan na tambayi dalibai na 'yan shekarar farko a jami'a abin da suka sani game da mulkin mallakar da Jamus ta yi, me kuka koya a sakandare? Akwai wani rukuni da bai san komai a kai ba, akwai wadanda ke da cikakkiyar masaniya, musaman game da kisan kare dangi na Herero. Idan ka tambaye su dalilin aikata ta'asar, to a nan kuma gizo ke saka."
Ita ma 'yar Namibiya kuma daraktar cibiyar nazarin dimukuradiyya, Naita Hishoono ta yi korafin cewa har yanzu a Jamus ba kasafai ake batun mulkin mallaka ba, ba ya kuma taka rawar a zo a gani a siyasar kasar. Ta yi nuni da tattaunawar da aka fara tun a 2015 tsakanin Jamus da Namibiya, kan bayar da diyya ga kisan kare dangin da Jamusawa 'yan mulkin mallaka suka yi ga kabilun Herero da nama, batun da har yanzu ba a samu matsaya ba.