1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ministocin kungiyar G7

Suleiman Babayo MAB
November 8, 2023

Taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G7 ya bukaci tsagaita wuta a yankin Zirin Gaza na Falasdinu domin samun kai kaya agaji na taimakon fararen hula da rikicin Isra'ila da Hamas ya ritsa da su.

https://p.dw.com/p/4Ya0Z
Kayan agaji zuwa Gaza
Kayan agaji zuwa GazaHoto: AMR ABDALLAH DALSH/REUTERS

Ministocin harkokin waje na gaggan kasashe masu arzikin masana'antu na duniya na G7 sun bukaci samar da tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas domin shigar da kayan agaji yankin zirin Gaza da batun sakin 'yan Isra'ila da ake garkuwa da su. Ministocin wadanda suke taro a birnin Tokyo na kasar Japan sun bayyana haka lokacin wata sanarwar da suka cire.

Kasashen wadanda suke sahun gaba wajen karfin tattalin arziki tsakanin kasashen duniya sun jadada bukatar Isra'ila ta kare kanta daga tun wata barazanar tsaro, amma sun bukaci samun lafawar bude wuta domin taimakon fararen hula.