1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Netantahu ya kammala ziyarar da ya kai a Afirka

Salissou BoukariJuly 7, 2016

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya kammala ziyarar da ya kai a wasu kasashen Afirka hudu, da suka hada da Yuganda, Kenya, Ruwanda da kuma Habasha.

https://p.dw.com/p/1JLQs
Äthiopien Addis Ababa Benjamin Netanjahu Staatsbesuch Hailemariam Desalegn
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da takwaransa na Habasha Haile Mariam DessalegnHoto: DW/Y. Gebereegziabahre

A karshen ziyarar tashi A wannan Alhamis din, Netanyahu ya yi jawabi a gaban 'yan majalisun dokokin kasar ta Habasha inda ya ce, muna masu gani a zahiri irin mahimman abubuwa masu babban amfani da kasar Habasha da ma Afirka suka kumsa, kuma yana mai cike da farin cikin sanar musu cewa Isra'ila na da babban buri ga kasashen Afirka a fannoni da dama.

Wannan ziyara dai ta wani shugaban gwamnatin Isra'ila da ke zaman irinta ta farko a kasashen na Afirka da ke Kudu da Sahara, ta zamanto wani abun tarihi a cewar Firaministan na Isra'ila. A shekara ta 1960 ne dai kasashen Afirka da dama suka soma raba gari da Isra'ila sakamakon yakin da ta yi da makwabtanta Larabawa tsakanin 1967 zuwa 1973, sannan ga batun huldar kasar ta Isra'ila da gwamnatin wariyar launin fata ta Afirka ta Kudu.