Netherlands: An kama dubban masu kare muhalli
September 10, 2023Magajin garin Hague ya ce, jami'an sandan sun kama mutane kimanin 2,500. A kalla masu fafatukar 10,000 ne suka rufe babbar hanyan da ke zuwa birnin Hague na tsawon sa'oi a ranar Asabar. Ko a ranar Lahadin ma, jami'an 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar bisa zargin rashin yinta a babban tashar birnin kamar yadda aka ba su damar yi tun da fari.
Masu rajin kare muhallin dai na zanga-zanga ne domin nuna adawa da matakin gwamnatin kasar na bada tallafi ga kamfanonin da ke samar da makamashin da ke fitar da hayaki mai gurbata muhalli kamar yadda suka yi watannin baya-bayan nan.
Gwamnatin Netherlands dai ta ware tallafin fiye da dala milliyan 40 a kowace shekara ga kamfanonin, sai dai masu fafutukar na cewa, ba za su daina adawa da hakan ba har sai gwamnati ta daina tallafawa kamfanonin mai da iskar gas da kudin al'umma.