1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Netherlands za ta fita daga yarjejeniyar yan gudun hijira

Abdullahi Tanko Bala
September 18, 2024

Gwamnatin Netherlands ta hadakar 'yan ra'ayin rikau ta sanar da aniyarta ta shirin fita daga yarjejeniyar kungiyar tarayyar Turai kan yan gudun hijira da yan cirani.

https://p.dw.com/p/4koMW
Ministar kula da neman mafaka da yan gudun hijira ta kasar Netherlands Marjolein Faber
Hoto: Remko de Waal/ANP/IMAGO

Matakin na zuwa ne bayan da gwamnatin ta sanar da tsauraran manufofi kan shige da fice.

A wani sako da ta wallafa a shafin sada zumunta na X Ministar kula da neman mafaka da kaurar jama'a Marjolein Faber ta ce ta sanar da hukumar tarayyar Turai cewa kasar Netherlands na bukatar janyewa daga batutuwan da suka shafi kaurar jama'a.

Ta ce za su aiwatar da nasu tsarin na manufofin neman mafaka.

Kafin kasar ta Netherlands ta iya fita daga yarjejeniyar baki daya sai ta sami amincewar dukkan mambobin kasashe 27 na kungiyar tarayyar Turai EU.