1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An baza sakamakon binciken a kan kafofin sada zumunta

Salissou Boukari AH
May 26, 2020

Takaddama ta sake kunno kai kan batun sama da fadi da wasu ‘yan kasar suka yi da dukiyar kasa a ma’aikatar tsaron kasar, inda a halin yanzu rahoton binciken ya bayyana a kafofin sada zumunta na zamani.

https://p.dw.com/p/3cmiL
Niger Bewaffnete Drohne in Niamey
Hoto: picture-alliance/AP Photo/French Defense Ministry/M. Buis

Sannu a hankali dai za a iya cewa abin da ke cikin duhu na kara fitowa fili dangane da batun badakala da aka yi a ma’aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar, inda wasu mutane kama daga ‘yan kasuwa, da ma manyan ma’aikatan da ke wannan ma’aikata suke da hannu kan sama da fadi da aka yi na dubban miliyoyin CFA a kasar da kusa a kullu yaumin take tara hannu ga kasashen waje domin kawo mata tallafi a fannoni dabam-dabam.  Musamman ma kasashe irin su Faransa, Jamus, Amirka, Beljiyam italiya da dai sauransu sun taka rawar gani wajen bayar da horo ga sojojin na Nijar, ko kuma samar da kayayakin aiki  a wani mataki na kara wa kasar ta Nijar karfi. Sai dai wallafa takardun binciken da aka yi a yanar gizo zai iya kawo sauyi ga tafiyar da wannan batu da a halin yanzu yake gaban shari’a. A halin yanzu dai ana iya cewa lamarin ya yi nisa, domin kuwa wata majiya na cewa tuni aka saurari da dama daga cikin wadanda sunayansu ko sunayan kamfanoninsu suka bayyana a cikin wannan bincike, inda aka tabbatar da dubban miliyoyin kudade na CFA da aka yi sama da fadi da su ta hanyar kamfanoni na jabu. Sai dai kuma a  cewar Moussa Aksar wani dan jarida mai bincike, kuma masani kan harkokin tsaro, shi dai ya kyautu a rika wallafa abin da ke na gaskiya, sannan shari’a ta yi aikinta idan ana son zaman lafiya.

Wani kusa a jam'iyyar PNDS Tarayya ya ce akwai karya a cikin wasu bayanan da aka wallafa

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Shugaban Nijar Mahamadou IssoufouHoto: AFP/I Sanogo

Da yake magana kan wannan ce-ce-kuce da ake yi musamman ma kan batun na ma’aikatar tsaron kasar ta Nijar, inda mutane ke ci gaba da wallafa takardun binciken, Assoumana Mahamadou wani kusa a Jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya cewa ya yi wasu abubuwan da ake wallafawa karya ce  kawai domin batun dai  na a hannun shari’a. Abin jira dai a gani shi ne hukunci da zai biyo baya, ganin cewa tuni yayin sauraron da ‘yan sanda masu bincike suka yi wasu sun amsa laifukansu, tare ma da shan alwashin biyan kudaden da aka tambayosu, yayin da wata majiyar ke cewa rahoton ma da ake yadawa ta yanar gizo ba wai na karshen ne ba, Sannan a cewar wata majiyar, kasashe da dama da ke da ruwa da tsaki kan harkokin tsaron kasar ta Nijar na bin lamarin sau da kafa.