Azumi cikin dokar hana cunkoso a Nijar
April 24, 2020Kafin zuwan watan azumin dai, al'ummar Jamhuriyar ta Nijar sun tsammaci za a sassauta matakan da aka dauka domin kariya daga Coironavirus din, musamman ma ganin yadda sannu a hankali masu kamuwa da cutar raguwa a kasar, koda ya ke a wasu lokutan adadin kan karu. Ganin cewa yaune al'ummar Jamhuriyar ta Nijar ta bi sahun sauran kasashe wajen tashi da azumin watan Ramadan din, wanda a cikinsu ake yawaita ayyukan ibada muamman ma salloli da addu'o'i da tafsirai.
Sau tari dai an sha samun dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaro da sauran al'umma masu neman yi wa dokar zaman gidan karan tsaye, alhali kuma su kansu malaman addini sun yi kira da a nesanci yin zanga-zanga ko fito na fito da hukuma musamman ma a wannan lokaci na azumin watan Ramdan.
Fatan kawo dauki da gyara
Imam Ustaz Aboubakar Ibrahim limamin Masallacin Jumma'a ne, ya ce fatansu shi ne ganin an duba wannan lamari na Masallatai tare da saka cikakken tsari a cikinsu. A wani taron manema labarai da ya kira a wannan Juma'ar, jagoran kungiyoyin fararen hula Nouhou Arzika ya yi kira ga magabata da su rinka daukar matakai na sassauci ga jama'a kamar yadda aka yi kan batun takaita zirga-zirga, tare yin kira ga jama'a da su dukufa ga yin addu'o'in fatan kawo karshen wannan masifa, tare da fatan ganin an sallamo abokansu 'yan kungiyoyin fararen hular da aketsare da su, domin su yi azumi cikin iyalansu.