Nijar: Jama'a ba su fita zabe ba sosai
March 20, 2016Rashin fitar mutane zuwa rumfunan zabe ya rage armashin zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Jamhuriyar Nijar idan ake takara tsakanin shugaba mai ci Issoufou Mouhamadou na jam'iyyar PNDS Tarayya da kuma Hama Amadou na jam'iyyar Moden Lumana Afirka wadda ke adawa. Jam'iyyar ta Lumana tare da sauran jam'iyyun adawa sun kauracewa zaben na yau saboda abinda suka kira rashin adalci da kusakuran da aka tafka a zagayen farko na zaben.
Masu aiko da rahotanni suka ce ba wani tashin hankali da aka fuskanta a zaben baya karancin fitar mutane ko da dai can yankin Maradi mutane da dama sun fita musamman ma dai a wuraren da jam'iyya mai mulki ke da magoya baya. A Tawa da Dosso da Damagaram da Yamai labarin ya sha banban don ba mutane a rumfunan zabe, har ma wakilinmu da ke Damagaram ya ce wasu mutane ma shi'anin kasuwancinsu suka fi maida hankali a kai maimakon zaben.
Shi dai wannan zagaye na biyu na zaben na shugaban kasa a Nijar na gudana a wasu kasashen duniya ciki kuwa har da Jamus da Beljiyum da Cote d'Ivoire da Najeriya. Wakilinmu da Kaduna a arewacin Najeriya ya ce zaben na gudana lafiya kuma mutane sun yi fitar dango don kada kuri'arsu fiye ma da yadda aka gani a wasu sassa da ke cikin Jamhuriyar ta Nijar.