1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar MNSD ta shiga gwamnatin Nijar

Mahamane Kanta/ SBAugust 14, 2016

Bayan dogon lokaci da aka dauka ana yada jita-jita kan wannan batu, ta tabbata cewa kwamitin koli na jam'iyyar MNSD Nassara mai adawa a Jamhuriyar Niyar ya yanke shararar shiga gwamnati.

https://p.dw.com/p/1JhzG
Niger Wahlen Seini Oumarou
Alhaji Seini Oumarou shugaban jam'iyyar MNSD Nassara a NijarHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Jam'iyyar ta MNSD Nassara karkashin jagorancin Alhaji Seini Oumarou da ke cikin kawancen jam'iyun adawa dai, ta amince za ta shiga gwamantin Shugaba Issoufou Mahamadou bayan kiran da shugaban kasar ya yi tayin kafa gwamnatin hadaka, cikin jawabinsa na bikin tunawa da ranar da Jamhuriyar ta Nijar ta samu 'yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka na Faransa. Jam'iyyar ta MNSD ta bayyana wannan kudiri nata ne dai bayan wani taron muhawara da wakilan jam'iyyar da suka fito daga jihohin kasar suka gudanar a Yamai babban birnin kasar, inda mambobin kwamitin kolin jama'iyyar 148 daga cikin 203 suka halarci taron, kana 144 suka amince da matakin.