Makomar 'yan majalisar dokoki da jam'iyyar MNSD ta kora
October 7, 2015A Jamhuriyyar Nijar, jam'iyyar MNSD Nasara da ke adawa ta kasance dunkulalla sakamakon hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a ranar Litinin da ta gabata, inda ta ba wa shugaban jam'iyyar Seini Oumarou gaskiya, in ban da wasu jiga-jiganta da suka yi wa jam'iyyar tawaye, suka kuma karbi mukamai a gwamnatin Shugaba Mouhamadou Issoufou.
Wannan dai ya sa uwar jam'iyyar ta kori wasu kusoshin jam'iyyar mutum 48. Daga cikinsu kuwa akwai 'yan majalisar dokoki 12 da suka hada da Amadou Salifou da ke zama shugaban majalisar dokoki. Dukkan wadannan mutanen dai yanzu haka ba su da wata jam'iyya.
To ko yaya makomar wadannan tsoffin 'ya'yan jam'iyyar ta MNSD? Honourable Sani Mai Goshi na daga cikin korarrun na jam'iyyar.
"Kundin tsarin mulkin kasa da kundin zaman majalisa sun tabbatar da cewa in jam'iyya ce ta fidda sunan dan majalisa, dan majalisar zai ci gaba da zama a matsayin dan majalisa, amma mai zaman kanshi ba dan jam'iyya ba. Saboda haka tun da mun amince da abinda kotu ta tabbatar da shi, mu 'yan majalisa ne na kasa sai mun ida mandat dinmu kaf. Amma muna zaman kanmu."
Matakin da za a iya dauka kan sauran 'yan tawayen jam'iyya
Daga cikin 'ya'yan majalisar 12 da suka yi wa jam'iyyar ta MNSD tawaye, guda tara ne korar ta shafa, amma ban da sauran ukun. Murtala Mamoudou na zama daya daga cikin shika-shikan jam'iyyar cewa ya yi.
"Matakin bai taba su ba amma yanzu dole ne jam'iyya ta yi zama kansu, tun da ba a fidda su ba. Har yanzu su 'ya'yan jam'iyya ne babu wani hukuncin da aka yi musu. Laifinsu shi ne ba sa shiga cikin harkokin jam'iyya. Za a jira a gani ko za su yi wa kansu kiyamun lailu su dawo cikin jam'iyyar ko kuma za su ci gaba da harkokinsu ne. Idan suka dawo suka yi nadama, za a duba wannan kafin a san mataki na gaba da za a dauka."
Ayar tambaya kan makomar kusoshin jam'iyya
To yaya makomar shi kanshi shugaban majalisar dokoki Amadou Salifou wanda da bazar ta jam'iyyar MNSD Nasara ce aka zabe shi kan wannan mukami? Dr Boukari Amadou Hassane malami ne a sashen ilimin tsarin dokokin kasa a jami'ar birnin Yamai ya yi fashin baki.
"Wannan ba ya hana Amadou Salifou zama shugaban majalisar dokoki. In kuna tune a lokacin da tsohon shugaban majalisa Malam Hama Amadou ya fita daga cikin gungun masu rinjaye, wadanda suka saka ayar tambaya game da halascinsa na shugaban majalisa, sun tambayi ra'ayin kotun koli mai kula da tsarin mulki. Wannan kotu ta ba da ra'ayi da cewa ba dole ne mai rike da shugabancin majalisa ya zama daga bangaren masu rinjaye ba. Duk dan majalisa na iya zama shugaban majalisa matsayar 'yan majalisa sun zabe shi ya ja ragamar wannan majalisa."
Wannan sabuwar dambarwar siyasa dai na ci gaba da daukar hankalin jama'a a Jamhuriyar ta Nijar domin ana yada jita-jita cewa bangaren Albade Abouba zai kafa sabuwar jam'iyya a daidai lokacin da zabukan kasar ta Nijar ke kara karatowa.