Nijar: Sakin talala ga wadanda ake zargi da juyin mulki
March 25, 2017Alkali mai bincike ya yi wa wadannan mutane sakin talala bayan da ya nazarin laifukan da ake zarginsu da aikatawa. Wakilinmu na birnin Yamai Abdoulaye Mamane Amadou ya tattauna da Maitre Ali Kadri lawyan da ke kare wasu daga cikin 'yan siyasar da aka zarga da juyin mulkin, wanda ya tabbatar da wannan labari, inda ya ce cikin 'yan farar hullan akwai 'yan majalisa biyu.
Sannan lawyan ya ce sakin na talala ne kafin a je ga shari'a ko ma da y ke ya ce bai san lokaci da za a je ga wannan shari'a ba.
Tun dai a ranar 17 ga watan Disamban na 2015 ne a wani jawabin da ya yi albarkacin bukukuwan zagayowar cikar shekaru 57 da samun mulkin kan kasar ta Nijar, Shugaba Issoufou Mahamadou ya sanar da cewa wasu gungun mutane sun yi yunkurin kifar da gwamnatinsa.