Nijar: Sauya tunanin matasa masu son zuwa Turai yin ci-rani
June 22, 2016Dan shekaru 30 da haihuwa Malam Islaman Abdou na daya daga cikin matasan da suka rungumi shafufukan intanet ko na sada zumunta wajen yada akidun irin su kamun kai da dogaro da kai da kwana da sanin cewar fa su ne manyan gobe. A jamhuriyar Nijar musamman ma a manya-manyan birane fasahar zamani na samun karbuwa saboda hakan ne ma yasa ayyukan Islaman Abdou suka dukufa wajen sauya tabi'un 'yan uwansa matasa ta hanyar nau'o'in sakwanni ta hanyar shafufukansa na sada zumunta ga wadanda suke da sha'awa da marmarin zuwa kasashen Turai ta ko wace hanya.
Yace: "Duk abinda nike yi daga farko shi ne waye kan 'yan uwanmu matasa don su san da cewar Turai din nan fa ba aljana ba ce. Gara ka zauna garinku ka kama kanka don samun abinda kaci."
Ba tun yau ba dai dan tahalilin ke aiki tukuru don wayar da kai ga matasa 'yan uwansa don ganin kasar Nijar da ma wasu kasashen Afirka sun rage radadin hasarar 'ya'yansu da ke hallaka a fannin shiga kungiyoyin ta'addanci da ma sauran da ke hallaka a teku a manufofinsu ta zuwa kasashen Turai.
Ya ce: "Na je har wajan su Agadez da Arlit na hadu da wadanda suke tasowa daga kasashen Senegal da Gambia da sauransu wai don zuwa Turai. Akwai wadanda sun zo kudinsu sun kare, wasu kuwa sun bada kudi mutumin ya gudu hakan abin yake."
Taruka da matasa da ke neman zuwa ci-rani
A kowace ranar Allah Ta'ala dai hakan Islaman Abdou ke shafe tsawon lokaci yana tabka mahawara da matasa da ke neman karin bayani ko wadanda suke son samun bayani kan labarun da yake wallafawa.
Ko baya ga shafuffukansa ma matashin na samun ziyarar 'yan uwansa matasa da ke saha'awar zama da shi don tattaunawa. Malam Mahaman Nasi wani matashi ne da ya je a dakin da Islaman Abdou yake aiki.
Ya ce: "Shi wannan aikin da wannan matashin yake yi a gaskiya aikin kwarai ne idan har akwai wadanda za su rinka taimakamashi to zai yi kyau sosai don a kwatanta wa wadanda suke aikin ketarawa zuwa kasashen waje da ba aikin kirki ba ne."
Sai dai duk da wadannan nasarori Malam Islaman Abdou ya ce akwai wasu tarin matsalolin da yake fuskanta kamar tsadar farashin sadarwa da rashin kulawa daga bangaren gwamnati da kuma rikon sakainar kashi da gwamnati take yi wa fannin matasan kasar.