Nijar: Shirye-shiryen babban zabe
Al'ummar Jamhuriyar Nijar za su kada kuri'a a ranar 27 ga watan Disamba, 2020, inda za su zabi shugaban kasa da 'yan majalisun dokoki. Zaben da ke zuwa cikin tarin kalubale na rashin tsaro da kuma annobar COVID-19.
Nijar: Zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki
Shekaru biyar bayan kada kuri'unsu, al'ummar Jamhuriyar Nijar za su sake zabar sabuwar gwamnati a babban zaben kasar da zai gudana a ranar 27 ga wannan wata na Disamba. Cikin watan Fabarairun 2021, za a rantsar da sabuwar gwamnati, da za ta kwashe tsawon shekaru biyar a kan karagar mulki.
Kalubalen rashin tsaro
Jamhuriyar Nijar na fuskantar kalubale da dama da suka hadar da na rashin tsaro. Kamar makwabtanta Najeriya da Kamaru da Chadi da Burkina Faso da Mali, kasar na fama da hare-haren 'yan ta'addan Boko Haram da ma na IS. Koda a baya-bayan nan ma, wani harin 'yan tadda ya halaka wasu Faransawa masu yawon bude ido a gandun dajin Koure, da ke da nisan kimanin kilomita 60 da Yamai babban birnin kasar.
Zabe cikin annobar coronavirus
Kamar sauran kasashen duniya, a Jamhuriyar Nijar ma ana fama da matsalar annobar cutar coronavirus da ta mamaye sassan duniya. A baya al'ummar Nijar, sun kaurace wa asibitoci sakamakon bullar annobar COVID-19 a kasar, abin da ya sanya mahukuntan kasar yin shela cikin watan Mayu dangane da bukatar al'ummar da su koma ziyartar asibitocin.
Mika mulki daga gwamnatin farar hula zuwa farar hula
Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar, zai zamo shugaba na farko da zai mika mulki daga gwamnatin farar hula zuwa wata farar hula, bayan ya kammala wa'adin mulkinsa na biyu. A watan Fabarairun shekara mai zuwa ta 2021 ne, wa'adin mukinsa na biyu zai kare, kuma a wannan lokaci zai mika mulki ga wanda ya lashe zaben da za a gudanar a ranar 27 ga watan Disamba na 2020.
Rawar kotu a zaben Nijar
A Jamhuriyar Nijar kotu na taka muhimmiyar rawa wajen tantance 'yan takara. Kotun tsarin mulki ce ke da alhakin amincewa da 'yan takara bayan sun mika takardunsu domin tantancewa. A bana daga cikin 'yan takarar shugabancin kasa a Jamhuriyar ta Nijar 41 da suka ajiye takardun takararsu, an yi watsi da takarar mutane 11 ciki har da babban madugun adawa Hama Amadou.
Babban madugun adawa da bai yi nasara ba
Hama Amadou jagoran adawa. Ya yi firaminista a shekara ta 1995 zuwa 1996 da kuma shekara ta 2000 zuwa 2007. Ya zama shugaban majalisar dokoki a 2011, ya koma adawa a 2013. Ya yi gudun hijira a 2014 sakamakon zarginsa da safarar jarirai. An yanke masa hukuncin zaman kaso a 2017. Ya tsaya takara a jam'iyyarsa ta Lumana Afirka bayan gwamnati ta yi masa afuwa, amma kotu ta yi watsi da takardunsa.
Tsohon shugaban kasa ya samu goyon bayan babbar jam'iyyar adawa
Zababben shugaban kasa na farko kana na hudu a tarihin Jamhuriyar Nijar, Mahamane Ousman ya sake tsayawa takara a karkashin jam'iyyar RDR Canji. Bayan zabarsa a 1993, an yi masa juyin mulki a 1996. Ya yi ta tsayawa takarar shugaban kasa bai samu nasara ba. Ya yi shugaban majalisar dokoki daga 1999 zuwa 2009. Bayan hana dan takararta, babbar jam'iyyar adawa ta Lumana Afrika ta mara masa baya.
Dan takarar da ba dan kasa ba?
Mohamed Bazoum dan takarar jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya. Ya fuskanci kalubale daga 'yan adawa da suka shigar da kara a gaban wata kotu a Diffa, suna zargin cewa shi ba dan kasar ba ne. Akasin madugun adawa Hama Amadou tsohon ministan cikin gidan ya tsallake siradi, domin kuwa kotun tsarin mulkin kasar a Yamai ta amince da takararsa, gabanin korar karar hadakar 'yan adawar a kotun Diffa.
Dan adawa da ya fice daga gwamnati
Ibrahim Yacouba ya taba zama ministan harkokin kasashen waje a 2016 zuwa 2018. Kafin nan, ya rike mukamin ministan sufuri a shekara ta 2012 karkashin jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki. Ya samu matsala da wasu shugabannin jam'iyyar, inda aka kore shi daga cikinta a 2015. Ya kafa tasa jam'iyyar mai suna MPN Kishin Kassa a 2015. Ya tsaya takara a 2016 bai samu nasara ba, yanzu ya sake tsayawa.
Tsohon na hannun daman Tandja
Albadé Abouba ya kasance ministan cikin gida har sau biyu lokacin mulkin marigayi tsohon shugaban kasar Tandja Mahamadou. Bayan juyin mulki an tsare su tsawon lokaci shi da Tandja. Ya zama minista na musamman a fadar shugaban kasa da kuma ministan gona a gwamnati mai ci ta Mahamadou Issoufou. Bayan wani rikicin cikin gida a jami'yyarsa ta MNSD Nasara ya fice, sun kuma kafa jam'iyyar MPR Jamhuriya.
Matasa sun tsaya takara
Mai shekaru 38 a duniya, Salim Salim Zanguina na daga cikin matasan Jamhuriyar Nijar da suka tsaya takarar shugabancin kasa a zaben na bana. Sai dai Salim Salim kamar Hama Amadou yana daga cikin wadanda ba su tsallake siradin kotun tsarin mulki na amincewa da 'yan takara bayan tantance su ba.
Rawar kungiyoyin farar hula
Nouhou Arzika na daga cikin 'yan kungiyoyin fararen hula da ke taka muhimmiyar rawa a al'amuran siyasa da ma na yau da kullum a Jamhuriyar Nijar. Sun yi ta fadi tashi dangane da batun dokokin zabe. Shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam ta MPCR, Nouhou Arzika na daga cikin 'yan farar hula da ke shan kamu daga mahukunta a Jamhuriyar Nijar.
Boren dalibai da yajin aikin malamai
Gwamnatin Mahamadou Issoufou ta sha fama da boren daliban jami'o'i. A cikin mulkinsa na tsawon shekaru 10, an yi ta samun boren daliban, inda ma aka zargi jami'an tsaro da halaka wani dalibi a jami'ar Abdoul Moumouni da ke Yamai fadar gwamnatin kasar. Malaman jami'o'i da ma na sauran makarantu musamman 'yan kwantiragi, sun yi ta tafiya yajin aiki.