Dakatar da amfani da ajujuwan zana a makarantun yara a Nijar
November 19, 2021Gwamnan birnin na Yamai Malam Oudou Ambouka ya kira taro na masu ruwa da tsaki kan harkokin ilimi domin yin bitar adadin ajujuwan zanan da ke da akwai a cikin birnin, musamman a makarantun kananan yara, da kuma daukar matakan gaggawa na samar da sabbin ingantattun ajujuwa ga kananan yaran da aka cire daga na zana a bisa umurnin gwamnatin Nijar kamar dai yadda gwamnan ya bayyana a lokacin bude zaman taron.
"Tun bayan iftila'in da ya wakana a Jihar Maradi, gwamnati ta dauki matakin dakatar da amfani da ajujuwan zana a makarantun kananan yara a kasa baki daya. Wannan mataki ne mai muhimmanci, kuma umurni ne mai karfi da aka ba mu, da ya zama dole mu yi biyayya gare shi."
Karin bayani: Nijar: Gobara ta halaka dalibai a makaranta
Binciken farko dai ya nunar da cewa akwai ajujuwan zana kusan 400 a fadin birnin daga ciki kimanin 60 na kananan yara. Malam Ibrahim Nalado mataimakin shugaban kungiyar iyayen yara 'yan makaranta ta kasa baki daya, daya daga cikin mahalarta taron da gwamnan ya kira, ya yi karin bayani kan matakan gaggawa da taron ya dauka na tunkarar wannan matsala da ta shafi kananan yaran 'yan makarantun reno.
"Ajujuwa 60 ake bukata cikin gaggawa, idan ba a samu ba, dole yaran za su koma gida. Ba ma son yaran su koma gida tun da ba mafita ba ce."
Bangarori da dama ne dai da suka hada da makarantu masu zaman kansu na cikin birnin na Yamai suka fara bayar da tasu gudunmawa ta samar da ajujuwan ga kananan yaran a cikin gaggawa domin ba su damar ci gaba da karatunsu.
Karin bayani: Nijar: An yi Jana'izar dalibai 27 da suka rasu a gobara
Mahukuntan birnin na Yamai sun kuma yi kira ga kamfanonin salula da bankuna da sauran masu hannu da shuni da su kawo tasu gudunmawa ta ganin an samar da ingantattun ajujuwan da ake bukata domin maye na zana da ke da akwai a illahirin makarantun birnin nan da 'yan shekaru.
Wasu alkalumman kididdiga sun nunar da cewa akwai ajujuwan zana kimanin dubu 36 a fadin Nijar. Kuma
dan kudin gina ingantaccen aji daya na tashi miliyan bakwai na CFA kamar yadda kwararru suka nunar, to kuwa gwamnatin Nijar na bukatar kudi tsaba miliyan dubu 250 na CFA domin maye gurbin illahirin ajujuwan zana na kasar da ginannun ajujuwa.