1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sojoji za su mika Bazoum wa kotu

August 14, 2023

Majalisar sojojin da ta yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar ta sanar da aniyar gurfanar da hambararren shugaba Mohamed Bazoum a gaban kuliya domin tuhumarsa da laifin cin amanar kasa.

https://p.dw.com/p/4V7pX
Hoto: Facebook/Präsidentschaft der Republik Niger

A cikin wata sanarwar da ta fidda da Yammacin Lahadi, majalisarta ta CNSP karkashin Janar Abourahamane Tiani ta ce i zuwa yanzu ta tattatara dukannin hujjoji a kan hambararren shugaban da shi da 'yan amshin shatanshi na ciki na wajen kasar domin tuhumarsu a gaban kotuna na kasar da kuma na kasa da kasa bisa aikata wannan babban laifi.

Sannan majalisar ta sha alwashin ci gaba da rike sauran membobin gwamnatin da ta kifar amma cikin mutumta tanade-tanaden dokokin kasa da kasa da suka jibancin kare hakin dan Adam wadanda da Nijar ta rattaba. 

Daga karshe majalisar ta yi Allah wadai da takunkuman da ta alakanta da na rashin imani da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika ECOWAS ta kakaba wa Nijar ciki har da hana shigo da magani da kayan abinci da kuma katse wutar lantarki da ta ce na kara wa talakawan kasar radadin ukubar da suka share tsawon shekaru a ciki.