1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sojoji na zargin Faransa da karya doka

August 9, 2023

Majalisar mulkin soji a Nijar ta zargi Faransa da ke zama uwargijiyar kasar da sakin wasu 'yan ta'dda tare da karya dokar kasar na ketara sararin samaniyarta.

https://p.dw.com/p/4UyC1
Hoto: REUTERS

Sojojin da suka kwace mulki a hannu gwamnatin fararar hula sun zargi gwamnatin Faransa da sakin 'yan ta'adda da ake tsare da su, wadanda ke da hannu cikin matsalar tsaron da kasar ke fama da ita fiye da shekaru takwas. A cikin sanarwar da jagororin sojin suka fitar, sun ce 'yan ta'addan sun shirya kai hari kan sansanonin soji da ke kan iyakar Nijar da kasashen Burkina Faso da kuma Mali.

Sanarwar ta kuma bukaci hukumomin tsaro su kasance cikin shirin ko ta kwana yayin da suka bukaci jama'a su sanya ido kan lamuran da ke wakana a cikinsu.

Majalisar mulkin sojin Nijar din ta kuma zargi Faransa da keta sararin samaniyarta da jirgin yaki daga Chadi, wanda hakan ya saba wa dokar rufe sararin samaniyar Nijar din. Sai dai kuma gwamnatin Farasar ta musanta dukannin zarge-zargen.