Barazanar kashe Bazoum daga sojoji
August 10, 2023Kamfanin dillancin labaran Amurka na Associated Press ya ruwaito cewa, wakilin sojajin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar ta Nijar, ya shaidawa karamar sakatariyar harkokin kasashen ketare ta Amurka Victoria Nuland hakan yayin wata ziyara da ta kai Nijar din. Duk wani mataki na sasanta wa da sojojin dai ya ci tura, inda suka hana kowa ya samu damar ganin jagoran juyin mulkin. Ita kanta Nuland ba a amince ta ga jagoran juyin mulkin ko hambararren shugaban ba lokacin ziyarar tata, yayin da aka ki amince wa wakilan Majalisar Dinkin Duniya da na kungiyar Tarayyar Afirka AU da ma na kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO zuwa kasar baki daya. Ko da yake an hango jagoran juyin mulkin Abdourahmane Tchiani yana ganawa da Sarkin Kano na 14, kana shugaban darikar Tijjaniya Khalifa Muhammad Sanusi na II da ya jagoranci wata tawagar Najeriya zuwa Yamai.