1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da kyamar Faransa a Sahel

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 4, 2023

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun bayyana yanke alakar soja da Uwargijiyarsu Faransa da ta yi musu mulkin mallaka.

https://p.dw.com/p/4Un4h
Jamhuriyar Nijar | sojoji | Kyama | Faransa
Dubban 'yan Nijar din dai, sun yi zanga-zangar nuna kin jinin FaransaHoto: Mahamadou Hamidou/REUTERS

Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar din, sun kuma yi gargadi ga kasashen Afirka ta Yamma da su sanya idanu kan sojoji da kuma masu leken asiri daga kasashen ketare. Sanarwar da jagororin juyin mulkin na Nijar suka yi a kafar talabijin din kasar, ta nuna karara yadda suke kokarin yin watsi da duk wani abu da ke da alaka da Amurka da kawayenta a yankin Sahel, yanki mafi girma a Saharar da masu tsattsauran ra'ayin addini suka mayar tungar 'yan ta'adda. Hambararren shugaban kasar Jamhuriyar ta Nijar Mohamed Bazoum da ke rike hannun sojojin da suka kifar da agwamnatinsa, yayi kira ga Amurka da kawayenta su taimaka wajen kwato shi. Kiran nasa na zuwa ne kwanaki biyu kafin cikar wa'adin da kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ko CEDEAO ta dibarwa sojojin, na su sake shi su kuma mayar da shi kan madafun ikon da suka kwace.