Nijar: Yaki da cin hanci a sahun 'yan sanda
November 1, 2018Bincike da hukumar yaki da cin hanci da rashawa tare hadin gwiwa da hukumomin Nijar suka aiwatar ya tabbatar da cewa masu sanye da kaki ko damara ta jami'an tsaro na kasancewa a matsayin na gaba-gaba wajen karbar na goro da ma cin hanci daga jama'a. Batun da kuma babban jami'in na kungiyar matuka motocin daukar fasinja Seidou Yacouba ya ce abin ya fara zaman na fitar hankali.Ya ce: ''A cikin kasashen Afirka ta yamma cin hanci Nijar ya fi kamari a nan Makolondi 'yan Nijar masu zuwa ci rani da ke fitowa da takardunsu to amma kuma kowa sai ya bayar da kudi, haka idan za su dawowa a gidajensu sai sun biya kuma babu wani dalili.
Wadannan na daga cikin wasu mahimman dalilan da suka kai ga gwamnatin Nijar tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi na kasa da kasa musamman GIZ da Cooperation Allemande ta kasar Jamus tattaro daukacin jami'an tsaron kasar domin tantance musu illolin da ke tattare da wannan mummunar akida da ke neman samun gindin zama a bainar jami'an tsaro na kasa.