Dubban magoya bayan 'yan adawa sun amsa kira a Yamai
November 11, 2018Talla
Tsohon shugaban kasar ta Jamhuriyar Nijar Alhaji Mahamane Ousmane ne dai ya jagorancin wannan zanga-zanga wadda wasu ke fadin ba'a taba ganin irinta ba daga cikin jerin zanga-zangar da 'yan adawan ke shiryawa a birnin na Yamai. Wani kudiri ne dai mai lamba takwas na kundin zaben kasar ta Jamhuriyar Nijar ke kan gaba wajen haddasa cecekuce a kasar. Wannan kudiri kuma ka iya haramta wa madugun 'yan adawan kasar Hama Amadou tsayawa takara a zabukan kasar masu zuwa abin da 'yan adawar na Nijar suka ce ba za ta sabu ba.