Tillabéri na fama da harin 'yan ta'adda
March 17, 2021Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam a Jamhuriyar ta Nijar, suka fara tofa albarkacin bakinsu dangane da yadda matsalar tsaro ke kamari a yankin na Tillabéri duk da matakan tsaron da gwamnati ke cewa tana dauka. A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin kasar Malam Zakariya Abdourahmane ya karanto a daren Talatar da ta gabata a gidan talabijin na kasa na Tele Sahel, ya ce maharan wadanda kawo yanzu ba a kai ga tantance su ba, sun tare wasu motoci hudu dauke da 'yan kasuwa da suka dawo daga cin kasuwar mako-mako ta garin Banibangouda kan hanyarsu ta koma wa garuruwansu na asali na Chinegodar da kuma Darey Dai.
Karin Bayani: Mummunan hari a Jamhuriyar Nijar
Kakakin gwamnatin ya kara da cewa, maharan sun sauko da su daga motoci tare da yi musu kisan dauki dai-dai bayan karbe musu dukiyoyi: "A kauyen Darai Dai maharan sun kashe mutane sun kuma kona rumbuna. A jumulce a cikin wadannan tagwayen hare-hare, mutane 58 sun halaka guda ya jikkata sun kuma kona runbunan abinci masu yawa da wasu motoci biyu kana sun yi awon gaba da wasu motocin biyu."
Yanzu haka dai mahukuntan na Nijar sun ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki uku daga wannan Laraba a duk fadin kasar. Sai dai Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasar ta Nijar irin su Alternative Espace citoyen ta bakin shugabanta Malam Moussa suka soma nuna damuwarsu da halin da ake ciki a Jihar ta Tillabery duk da matakn sojan da ake dauka a yankin.
Karin Bayani: Harin ta'addanci a barikin sojojin Nijar
Ita ma dai kungiyar MPCR ta Malam Nouhou Arzika ta bakin daya daga cikin shugabanninta Malam Nayoussa Jimraou a martaninta cewa ta yi, lokaci ya yi da ya kamata a zaunar da rukunnan kabilun jihar ta Tillabéri kan tebur domin gano bakin zaren warware matsalar. Gwamnatin ta Nijar dai ta sanar da aikawa da karin sojoji a yankin da kuma tsaurara matakan tsaro domin farauta mutanen da suka aikata wannan aika-aika da nufin kamo su a kuma gurfanar da su a gaban kuliya.