Neman a saki 'yan farar hula a Nijar
April 15, 2020Wadannan mutane da ke tsare dai, sun hadar da Moussa Tchangari shugaban kungiyar Alternative Espace Citoyen da Maikol Zody shugaban kungiyar Tournon la Page Niger da Moudi Moussa dan jarida kuma shugaban kungiyar Tournon la Page na birnin Yamai da Halidou Mounkaila shugaban kungiyar malaman makaranta ta CYNACEB kuma mamba a gamayyar kungiyoyin fararen hula masu fafutika. Sauran su ne Halidou Hassane mai kula da yada labarai na kungiyar Tournons la Page da kuma shugaban 'yan kasuwa masu shigowa da fitar da kayayyaki Sani Shekarau. Wadannan mutane dai ya zuwa yanzu sun cika kwanaki 30 a tsare.
Kafafen sada zumunta ne mafita
Ibrahim Yacouba shi ne shugaban gamayyar jam'iyyun na Front patriotique kuma shugaban jam'iyyar MPN Kishin Kasa, ya ce sun yi amfani da kafafen sada zumuntar na zamani ne domin kai kokensu, ganin cewa yanzu gwamnati ta hana duk wani tarp da zai haifar da cunkoson jama'a, a kokarin dakile yaduwar annobar Coronavirus da ta addabi duniya baki daya. Tuni dai 'yan kungiyoyin fararen hular suka yaba wannan fasaha da Front Patriotique suka fito da ita, domin ganin abokansu sun fito daga gidajen kaso da ake tsare da su.
Ko matakin ya dace?
Sai dai a cewar Alhaji Assoumana Mahamadou wannan lamari bai kamata ba ga duk wanda ya ce yana son a bar doka ta yi aikinta, domin kuwa tuni wannan batu ke gaban kuliya, inda ya ce duk wani azarbabi bai dace ba. Tsawon wadannan kwanaki dai da 'yan kungiyoyin fararen hular ke tsare, an ce babu wanda ya gansu da sunan kai musu ziyara, hakan kuwa na da nasaba da matakin da ofisin ministan shari'a na kasar ta Nijar ya dauka cewa an hana ziyarar har tsawon watanni uku, sakamakon annobar Coronavirus.