Nijar:Karfin soja ba zai magance tsaro ba.
June 16, 2022Tun daga shekarar 2011 da aka soma fuskantar matsalolin ta’addanci a kasar ta Nijar, bincike ya nunar da cewa kudadan da aka zuba da sunan samar da tsaro sun kasance ninki ba ninkin amma kuma har yanzu gidan jiya noman goge ko da ya ke a wasu wuraren kura ta lafa. Akasarin wadanda ke rayuwa a yankunan da ake fama da tashe tashen hankula na ganin ya kyautu a yi amfani da ilimi wajen shawo kan wannan matsala. Fatouma Torodi, wata 'yar kungiyar farara hula ce daya daga cikin jagorori masu fada a ji.
A can ma gundumar Gothey da Tera da ke cikin jihar Tillabery ana fuskantar wannan matsala ta tsaro wanda ko a cikin 'yan kwanakin nan a gundumar Gothey a garuruwan da ke kan iyaka da Burkina faso, an yi babbar arangama da jami’an tsaron Nijar da 'yan ta’adda masu manyan makammai kuma a cewar Morou Edo, na kungiyar farar hulla ta gundumar Gothey sai gwamnati ta sake dabara.
Wasu daga cikin mazauna yankin da ake fama da matsalar tsaron na ganin cewa ya kyautu a samar da jami’an tsaro isassu da za su tsare muhimman wurare sannan a gyaran inda 'yan ta’adda suka lalata da samar da ruwa da sauran ababen rayuwa kafin a yi batun mayar da mutane gidajensu. Sai dai a cewar Abas Abdoulmoumouni wani mai sharhi kan harkokin ta‘addanci da tsattsauran ra’ayi babban abun da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne na tarbiya ta gari.