Nijar: Sabon tsarin tallafawa ilimin yara mata
January 24, 2020Binciken ya nuna yadda a gundumar Tasawa da ke cikin jahar Maradi, dalibai 'yan mata masu yawa ne ake fidawa daga makarantun boko alhali suna cikin matukar bukatar cigaba da iliminsu, masarautar garin Tasawa ta assasa wani sabon tsari na mayar da wadannan matan makaranta domin su cigaba da karatunsu.
Sabon tsarin ya dauki nauyin mayar dasu makaranta, bayan sun kwashe wata hudu suna zaune a gidan iyayensu ba karatu ba aikin yi, Mai martaba sarkin Tasawa Malam Mansur Kane Mai Gizo shi ne ya assasa wanan tsari tare da tallafin hukumar majalisar dinkin duniya mai kula da bunkasa rayuwar mata UNFPA, a wani mataki na tallafama karatun yara mata musaman yaran talakawa wadanda basu da halin biya kudin karatu baya an fitar dasu daga makarantun gwamnati.
Kungiyar malaman makaranta ta yaba da tsarin na mai martaba, ta ce abin yabawa ne kuma abin koyi kamar yadda Musa Salay daraktan makaratun sakandary na gundumar Tasawa ya bayana .Dukanin shuganin gundumar Tasawa sun yi baki guda kuma sun dauki matakai dan cimma burin da tsarin ya sa a gaba.