Nishadi maimakon ta'addanci: Gidan adana namun daji na Maiduguri
An shafe shekaru 'yan ta'addadan Boko Haram na karkata yadda rayuwa za ta kasance a Maiduguri. Har yanzu suna kai hare-hare jifa-jifa, amma mutane sun sake samun farin ciki: Misali da yamma a gidan adana namun daji.
Giwaye masu neman toron giwa
Sunan giwayen Izge da Juma wadanda ke jan hankalin masu ziyara. Mustapha Pogura (na 2 daga hagu) ya fito daga Jihar Yobe mai makwabtaka, inda ya shafe wani lokaci da rana yana ziyara a gidan ajiye dabbobin: "A baya babu tabbas, amma yanzu akwai zaman lafiya a nan." Gidan adana namun dajin zai kara inganta idan aka zuba kudade, a cewar Pogura. Ma'aikatan suna son samun toron giwa domin giwayen.
Wajen hutawa da gidan dabbobi da ya shekara kusan 50
Da farko akwai masu kula da gidan na gargajiya inda mutane suka fara bayar da kyautar dabbobi a wajen adana motoci a 1970. A 1974 Jomo Kenyatta ya kai ziyara Maiduguri. Shugaban Kenyan ya kai nau'in dabbobin gabashin Afirka zuwa Najeriya. Daga nan wajen hutawar ya zama gidan adana namun daji. Amma sannu a hankali dabbobin suka rika mutuwa saboda shekaru ko kuma yanayin da ba su saba ba na zafi.
Inuwa da yanayin nishadi mai kyau a tsakiyar birni
Duk wanda ya biya Naira 50 (kimanin centi 10 na Euro) zai shiga wannan katafaren filin da aka kewaye mai girman hekta 17. Akwai shagunan da maziyarta ke sayen kayayyakin shaye-shaye. Galibin mutane suna zuwa da yamma lokacin da rana ke shirin faduwa. Manya kan zauna akan kujeru yayin da yara ke leken macizai.
Wajen yara
Khadija (a dama) daliba 'yar shekaru 15 ta kai ziyara tare da kawaye da 'yar uwarta Aisha (ta biyu daga dama). Zakuna suna cikin wadanda aka fi so a gidan adana namun dajin. Aisha tana murna da haka "Ina jin dadi akwai wuri mai kyau ga mu yara." Ana cika a karshen mako. Kuma ma'aikatan sun ce ana samun mutane sosai lokacin bukukuwa.
Gawurtaccen Zaki
Ga yaran da shingen karfe mai kauri ya raba da zakin suna yi masa ganin abin sha'awa. Zakin yana tare da zakuna mata biyu a wajen da suke killace. Amma lokacin da 'yan ta'adda suka farma birnin Maiduguri yana da wahala samun abincin da suke bukata a cewar rahoton masu kula da gidan adana namun dajin. Sai da aka yi amfani da akuyoyin gidan. Kuma Dabbobi da yawa masu cin nama ba su kai labari ba.
Kadodjin da suke tare
Kadojin sun saba rashin cin abinci na lokaci mai tsawo. Babu damuwa a Maiduguri. Ga alama suna cikin yanayi mai kyau a nan. Suna da yawa inda suke kewaye, saboda suna hayayyafa sosai. Yayin da ake ganin robobi a hotunan shekarun da suka gabata, yanzu dabbobin suna kan kasar da aka share.
Darakta yana da karfin gwiwa
Daraktan gidan adana dabbobin Usman Lawal yana aiki a wajen fiye da shekaru 20. Cikin alfahari ya nuna inda kadojin ke boye kwansu. "Farko gwamnati ba ta nuna kula ga gidan adana dabbobin" inji shi "Kana mun rasa dabbobi masu yawa." Amma gwamnan Borno na yanzu ya kara musu kasafin kudi. "Za mu inganta wajen da gyara wuraren gidan adana namun dajin."
Sabbin ofisoshi sabanin baya
Daraktan gidan adana namun dajin Lawal yana da gagarumin aiki a gaba. Godiya ga kudin da gwamnatin Borno ta samar da karuwar maziyarta, ana gina sabon ofishin gudanarwa wanda zai dauki ma'aikata 40, za kuma a kirkiro guraben aikin. Tuni aka fara sauya shingayen da aka killace dabbobi da sababbi.
Kura har yanzu tana jiran sabon gida
Inda aka killace kura yana tsallaken karamin kogi. Maziyarta kan isa wurin ta kan gada. Bayan ruwan abu kalilan ake gani na ginawa da sake gyara. Lallai kura tana jiran sabon gida, domin kejin da take ciki ya yi kankanta. Sau da yawa tana cikin dimuwa da kewaye wajen da gudu.
Sababbin dabbobi za su tabbatar da gaba
An kewaye jimina a wuri mai girma. Ba su dade a nan ba. Gwamna Kashin Shettima ya kawo su daga cikin nasa. Darakta Lawal yana son ganin dabbobin savanna kamar Jakin-dawa da Barewa. Kenya za ta sake taimako ke nan, Lawal yana da wannan fata: "Muna son tantubar mahukuntan birnin Nairobi kowanne lokaci nan gaba kadan."
Biri cikin tarkacen shara
Wani kalubale ga masu kula da gidan adana namun dajin shi ne maziyarta da ke saba dokoki. Wasu suna da halayyar jefa goruna da kwalaben ruwa ga birrai. Haka sharar ke zama. Tun shekara ta 2014 masana suka koka game da dabi'ar wasu maziyarta gidan adana namun dajin. Koda yake wajen ya daina zama wurin shan kwayoyi da haduwa da karuwai.
Birnin da ke fatan dorewar zaman lafiya
Gidan adana namun dajin yana kan hanyar da ta hada manyan titunan tsakiyar birnin. Yayin da ziyarar ta kasance cikin nishadi a birnin, harkokin yau da kullum na komawa kamar yadda aka saba. Amma a wajen birnin ana samun 'yan kunar bakin wake wadanda suke tunatar da mutanen Maiduguri cewa har yanzu da saura dangane da zaman lafiya.